logo

HAUSA

Shugaban Argentina: Na amince da shawarar shugaba Xi dake da nufin inganta ra’ayin kasancewar bangarori da dama

2023-01-21 20:39:20 CMG Hausa

Kwanan nan, yaduwar annobar COVID-19, rikicin dake tsakanin Rasha da Ukraine, daidaita manufar kudi da asusun ajiyar Amurka ya dauka daga gefe daya, da dai sauransu, sun kawo matsin lamba ga tattalin arzikin Argentina. A yayin da ake fuskantar sarkakiyar sauye-sauyen kasa da kasa, shugaban kasar Argentina Alberto Fernández ya bayyana a yayin da yake zantawa da ‘yar jaridar CMG a kwanan baya, cewa ya nuna matukar amincewarsa ga shawarar ci gaban duniya da ta tsaron duniya da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar.

Fernández ya ce, "A gani na, manufa mafi muhimmanci da kasar Sin ta gabatar ita ce girmama ra'ayin bangarori da dama, kuma muna goyon bayan irin ra’ayin. Ina adawa da nuna danniya ko babakere, kuma ba na son wata kasar dake nuna babakere ta wanzu a duniya. Shawarar da shugaba Xi ya gabatar, yana da nufin inganta ra'ayin kasancewar bangarori da dama da mutunta mulkin kai da halin musamman na kowace kasa. Ina mayar da hankali sosai kan wannan. Yaduwar annobar ta nuna rashin daidaito wajen ci gaban tattalin arzikin duniya. Lokacin da aka fara samar da alluran rigakafin COVID-19, an ba da kashi 90 cikin 100 na alluran duniya ga al'ummar da yawansu ya kai kashi 10% na duniya, wanda ke nuna rashin adalcin tsarin duniya. Kasashen Rasha da Sin sun kawo mana agaji da alluran rigakafi. Na yi imanin cewa, a duniyarmu ya kamata mutane su mutunta juna kuma kowa ya iya samun muhimman abubuwan da suke bukata kamar allurar rigakafi a yayin da ake tinkarar annoba. " (Mai fassara: Bilkisu Xin)