logo

HAUSA

Gwamnatin Najeriya ta musanta karin farashin mai

2023-01-21 15:32:55 CMG Hausa

Da yammacin Juma’a 20 ga wata, gwamnatin tarayyar Najeriya ta fito fili ta musanta rade-radin karin farashin man fetur.

Cikin wata sanarwar da karamin ministan ma`aikatar albarkatun man fetur na kasar Timipre Sylva ya fitar ta hannun mashawarcinsa kan sha’anin yada labarai Horatius Egua ta yi bayanin cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari bai ba da wani umarni na karin farashin man fetur ba.

Sanarwar ta ce, har yanzu shugaban kasa yana nan kan matsayinsa na cewa babu wani dalili da zai sanya a wannan lokaci da al’umma ke fuskantar kalubalen rayuwa sanadiyar matsalolin tattalin arziki a duniya kuma gwamnati lokacin guda ta yi karin farashin albarkatun mai.

Ministan ya ci gaba da cewa batun karin farashin mai, ba wai gwamnati kadai ce take yi ba sai ta zauna da manyan dillalan mai da sauran masu ruwa da tsaki.

Sanarwar ta ce wasu ne kawai masu son ta da zaune tsaye suka kirkiri wanann labari wanda ba shi da tushe ballantana makama, a don haka gwamnati ke kira ga ’yan Najeriya da su yi watsi da wannan jita-jita, tare da tabbatar da cewa ana nan ana kokarin kara samar da wadataccen man fetur a dukkan kasar baki daya. (Garba Abdullahi Bagwai)