logo

HAUSA

Najeriya da kasar Hungary za su hada karfi wajen fara kera jirgin yaki a Zaria dake arewacin kasar

2023-01-20 15:38:42 CRI

A ranar 18 ga wata yayin taron mako-mako na majalissar zartarwar kasar, ministan lura da harkokin sufurin jiragen sama na tarayyar Najeriya Hadi Sirika ya ce, gwamnati ta kebe Naira biliyan 2.29 ga kwalejin koyar da tukin jirgin sama dake Zaria a jihar Kaduna domin fara aikin har-hada jiragen yaki na soja.

Ministan ya tabbatar da hakan ne ga manema labarai dake fadar shugaban kasa jim kadan da kammala taron majalissar ministocin kasar.

Mataimakin shugaban tarayyar Najeriya Farfesa Yemi Osinbajo ne ya jagoranci zaman majalissar na wanann makon wanda aka zartar da batutuwa da dama da suka kunshi batun baiwa ’yan kasuwa hayar wasu manyan titunan kasar da kuma batun samar da cibiyoyin horas da ’yan sanda a dukkan sassan kasar.

Ministan sufurin jiragen saman ya ce Najeriya ta dade tana muradin kera kananan jiragen yaki masu inganci da juriya da za su dace da tsarin bayar da horo ga sojojin saman kasar dake neman kwarewa a fagen sarrafa jiragen, da ma su kansu direbobin jiragen fasinja.

Alhaji Hadi Sirika ya tabbatar da cewa kamar dai yadda aka tsara cikin ragowar watanni 4 da suka ragewa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari, jiragen farko da aka kera a kwalejin za su  fara tashi.

Ya ci gaba da cewa tun watanni 17 da suka gabata ne gwamnatin tarayyar Najeriya ta nuna sha’awarta ta hada karfi da kamfanin kera jiragen sama na kasar Hungry domin assasa kamfanin harhada kananan jirage ta amfani da fasahar gida.

Ya ce da zarar an fara aikin harhada jiragen a Najeriya to zuwa wani lokaci kalilan za a fara kera jiragen gaba daya, kuma an zabi kwalejin koyar da tukin jiragen sama ne dake Zaria ne a matsayin wurin da za a kafa kamfanin saboda akwai dukkannin kayayyakin da ake bukata a wajen, hakan kuma zai rage kashe kudade da yawa.

“Najeriya ai ba kasar wasa ba ce, Najeriya kasa ce babba mai arzikin yawan jama’a da ma’adanai da kima a idon duniya wanda tuni ya kamata a ce tana irin wannan kere-kere amma a ce Allura ko Ashana sai an kawo mana da wasu kasashe amma idan muka fara yanzu nan gaba ba abin da Najeriya za ta kasa kerawa har duniya wata ko na taurari ma ya kamata a ce Najeriya ta fara zuwa.”

Haka kuma majalissar ministocin ta amince da kashe Naira miliyan 546.11 domin sayo wasu na’urorin taimakawa jiragen sama sauka a yanayin da ake tsananin duhu ko hazo  ba tare da sun kauce hanya ba.

Daga Tarayyar Najeriya, Garba Abdullahi Bagwai. (Garba Abdullahi Bagwai)