logo

HAUSA

Lokaci Mafi Duhu A Sin Da Kafofin Watsa Labaru Na Kasashen Yammacin Duniya Suka Yi Hasashe, Ba Zai Tabbata Ba

2023-01-20 22:08:52 CMG Hausa

Bayan shekaru 3, an sake samun zirga-zirgar mutanen Sin masu komawa garuruwansu da yawa. Bisa kididdigar da aka yi, an ce, tun daga ranar 7 zuwa 18 ga wannan wata, yawan mutanen da suka yi zirga-zirga ta jiragen kasa, da jiragen sama, da jiragen ruwa, da motoci a kasar Sin, ya kai miliyan 480, wanda ya karu da kashi 47.1 cikin dari bisa na shekarar bara. Bikin baraza na bana, shi ne bikin na farko bayan da Sin ta kyautata matakan yaki da cutar COVID-19, inda aka fi samun farfadowa a zamantakewar al’ummar kasar Sin.

Amma wasu kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya sun yi hasashe ba tare da tushe ba, wai Sin ba ta shirya sosai wajen kyautata matakan yaki da cutar COVID-19 ba, inda suka ce bikin bazara na bana, zai kasance lokaci mafi duhu a kasar Sin a fannin tinkarar cutar.

A hakika dai, idan kasar Sin ba ta shirya sosai ba, ta yaya aka samu raguwar yawan mutanen da suke kamuwa da cutar COVID-19 mai tsanani a larduna daban daban na kasar, yayin da aka shiga kwana ta 11 da mayar da cutar COVID-19 zuwa rukunin B a kasar Sin. Sanin kowa ne cewa, akwai mutane fiye da biliyan 1.4 a kasar Sin. Idan kasar Sin ba ta shirya sosai ba, to me ya sa Sin ta fi samun karuwar mutanen da suke ci abinci a waje, da yin aiki a kamfanoni, da neman yin yawon shakatawa a kasashen waje? Kafofin watsa labaru na kasashen yammacin duniya sun zargi Sin a wannan fanni ba tare da tushe ba, kuma kowa ya san yunkurinsu. (Zainab)