logo

HAUSA

CMG ya gabatar da jerin sunayen shirye-shiryen shagalin murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin

2023-01-20 20:53:56 CMG Hausa

Babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya gabatar da jerin sunayen shirye-shiryen shagalin kade-kade da raye-raye da sauran wasanni masu ban sha’awa na murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin wato shekarar zomo.

Shagalin zai kunshi kade-kade da raye-raye, da wasannin kwaikwayo masu ban dariya, da wasannin gargajiya, da wasan Kungfu, da wasan yara da sauransu, wadanda za’a gabatar da su bisa fasahohin zamani da dama, a kokarin nuna kasar Sin mai jajircewa da ci gaba a sabon zamanin da muke ciki, da shaida yadda al’ummar kasar ke jin dadin rayuwarsu.

Da karfe 8 a daren ranar Asabar ne, CMG zai watsa shagalin kai tsaye, domin murnar shiga sabuwar shekarar gargajiyar kasar. (Zainab)