logo

HAUSA

Ana zargin mayakan 'yan aware da kashe jami'in zabe a Kamaru

2023-01-20 10:20:52 CMG Hausa

Wasu majiyoyin tsaro da na yankin kasar Kamaru sun bayyana cewa, wasu da ake kyautata zaton 'yan aware ne, sun kashe wani jami'in hukumar zaben kasar (Elecam) a yankin arewa maso yammacin kasar ta Kamaru mai magana da turancin Ingilishi.

Wani babban jami’in soja a yankin da ya bukaci a sakaye sunansa, ya shaidawa kamfanin dillanicn larabai na Xinhua ta wayar tarho cewa,‘yan ta’addar sun harbe Gilbert Yufola, shugaban hukumar Elecam a Jakiri, a daren Laraba a gaban gidansa dake Bamenda, babban birnin yankin.Yanzu haka dai, an baza jami’an tsaro suna sintiri a garin, ganin yadda zabe ke karatowa.

A ranar 12 ga watan Maris ne, za a gudanar da zaben 'yan majalisar dattijai ta Kamaru, amma 'yan awaren sun fitar da wata sanarwa ta kafar sada zumunta, inda suka gargadi kansilolin majalisun kananan hukumomi, dake zama manyan masu ruwa da tsaki a zaben, da su kaurace wa zaben, in ba haka ba za a kama su a tsare, ko kuma a halaka su.(Ibrahim)