logo

HAUSA

Sin Mai Bude Kofa Za Ta Kara Samar Da Dama Ga Duk Duniya

2023-01-20 20:51:59 CMG Hausa

Bude kofa ga kasashen waje da yin hadin gwiwa su ne muhimman manufofin diplomasiyya da kasar Sin ta gudanar a sabon zamani. Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi bayani sau da yawa ga duniya game da manufar Sin ta bude kofa ga kasashen waje, da ra’ayin Sin na sa kaimi ga raya tattalin arzikin duniya bisa tsarin bai daya, kana kasar Sin mai bude kofa za ta kara samar da dama ga duniya wajen samun ci gaba.

A shekarar 2022, yawan kudin shige da ficen kayayyaki na kasar Sin ya zarce kudin Sin Yuan triliyan 40 a karo na farko, inda ta kiyaye matsayinta na kasa ta farko da ta fi yin cinikin kaya a duniya a shekaru 6 a jere. Wannan ya shaida cewa, Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar bude kofa ga kasashen waje.

A ranar 18 ga watan Nuwanba na shekarar 2022, shugaba Xi Jinping ya bayyana a gun taron karba-karba na shugabannin kungiyar APEC cewa, a shekarar 2023, Sin za ta yi la’akari da gudanar taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar kasa da kasa na kasashe masu bin shawarar “ziri daya da hanya daya” karo na 3, don samar da gudummawa wajen samun ci gaba da wadata a yankin Asiya da tekun Pasifik da duk duniya baki daya.

A gun bikin baje koli na kayayyakin da ake shigar da su kasar Sin karo na 5, shugaba Xi Jinping ya kara bayyana manufar Sin ta fadada bude kofa ga kasashen waje don samar da damar raya tattalin arzikin duniya ta bude kofa.

Bisa rahoton bude kofa na duniya na shekarar 2022 da aka gabatar, Sin ta samu nasarori wajen bude kofa ga kasashen waje, inda ta kasance kasa mai muhimmanci wajen sa kaimi ga bunkasa tattalin arzikin duniya, kana ta sauke nauyin dake wuyanta na gabatar da damarmakin kasuwanni ga duniya da kuma sa kaimi ga farfado da tattalin arzikin duniya. (Zainab)