Xi ya mika gaisuwar bikin bazara ga daukacin Sinawa
2023-01-20 16:22:09 CMG Hausa
A yau ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, a madadin kwamitin koli na jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin (JKS) da majalisar gudanarwar kasar, ya mika gaisuwar bikin bazara ga daukacin al’ummar kasar Sin, a yayin wata liyafa da aka shirya a birnin Beijing, fadar mulkin kasar Sin.
Xi, wanda kuma shi ne babban sakataren kwamitin kolin JKS, kana shugaban rundunar sojojin kasar, ya gabatar da jawabi a wurin taron da aka shirya a babban dakin taron jama'a, inda ya gai da jama'ar kasar Sin na dukkan kabilu, da 'yan uwa dake yankunan Hong Kong, da Macao da Taiwan, da kuma Sinawa dake ketare.
Bikin bazara na bana ko kuma sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, ya fado ne a ranar 22 ga watan Janairu .(Ibrahim)