logo

HAUSA

Shugaban AU ya yi Allah wadai da sace mata da 'yan mata sama da 50 a Burkina Faso

2023-01-20 09:46:06 CMG Hausa

Shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Tarayyar Afirka Moussa Faki Mahamat, ya yi kakkausar suka kan sace mata da 'yan mata sama da 50 da aka yi a ranakun 12 da 13 ga watan Janairu a yankin Arbinda na yankin Sahel da ke arewacin Burkina Faso, da wasu da ba a san ko su wane ne ba suka yi garkuwa da su.

Wata sanarwa da kungiyar ta fitar a yammacin ranar Laraba, ta ruwaito Faki yana kira da a gaggauta sakin mata da ‘yan matan da aka sace, a kuma dawo da su cikin koshin lafiya zuwa ga iyalansu da ma al’ummarsu.

Ya kuma bukaci mahukuntan kasar, da kada su yi kasa a gwiwa wajen ganin an hukunta wadanda suka aikata wannan danyen aikin. Faki, musamman ya bayyana damuwarsa kan yadda kungiyoyi masu dauke da makamai ke kaiwa mata da 'yan mata hari a wani bangare na dabarunsu na cusa tsoro a cikin al’umma.(Ibrahim)