logo

HAUSA

Shirin bidiyo din na tallata shagalin murnar bikin bazara ya bayyana a wurare masu yawa na Turai da Amurka

2023-01-20 13:07:52 CMG Hausa

A ranar 18 ga watan Janairu, agogon wurin, an kaddamar da shirin bidiyo din na tallata shirin murnar bikin bazara da babban rukunin rediyo da talabijin na kasar Sin wato CMG ya tsara a cikin garin Rome, babban birnin kasar Italiya, inda aka fara share fage na ayyukan watsa labarai game da "Mu kalli shagalin murnar bikin bazara tare" na Turai.

A Burtaniya, a matsayin wani bangare na ayyukan murnar shiga sabuwar shekara ta gargajiyar kasar Sin, an nuna shirin bidiyon dake tallata shagalin murnar bikin bazara da CMG ya tsara a wurin taron manema labarai da ofishin jakadancin Sin a Burtaniya ya gudanar, wanda ya jawo hankalin jama'a daga sassa daban-daban na Burtaniya.

A yayin taron shekara-shekara na dandalin tattalin arzikin duniya na shekarar 2023 a birnin Davos na kasar Switzerland, shirin tallata din ya janyo hankulan wakilai mahalartan taron daga kasashe daban-daban.

Nan gaba, za a watsa shirye-shiryen musamman na bidiyo cikin harsuna da dama mai taken "Mu kalli shagalin murnar bikin bazara tare" a  manyan gidajen talabijin da kafofin watsa labarai na zamani sama da 60 a kasashen Italiya, da Sfaniya, da San Marino, da Serbia, da Arewacin Macedonia, da Albania da sauran kasashen Turai, kuma ana sa ran al’ummar Turai miliyan 80 za su kalli bidiyon.

Bugu da kari, a jajibirin bikin bazara, fim din dake talla shagalin murnar bikin bazara, zai isa gidajen sinima da na wasannin motsa jiki na kasar Amurka, wanda ya kawo kyakkyawan yanayi na bikin bazara ga jama'a da dama, kuma ya zama wani kyakkyawan dandamali na baje kolin al’adun bukukuwa da na gargajiyar kasar Sin. (Bilkisu Xin)