CMG zai kunna fitilu masu kyan-gani a husumiyar Burj Khalifa dake Dubai
2023-01-20 13:19:58 CMG Hausa
Babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko kuma CMG a takaice, ya tsara wani bikin kunna fitilu masu kyan-gani, daga bisani kuma a gabatar da shi a husumiyar Burj Khalifa dake birnin Dubai na Hadaddiyar Daular Larabawa, dake zama shahararren gini mafi tsayi a duniya, a gabannin bikin shiga sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin, wato a ranakun 20 zuwa 21 ga watan Janairu, da zummar isar da sakon gaisuwar kasar Sin ga dukkan fadin duniya.
Bikin bazara, ko kuma bikin murnar shiga sabuwar shekara bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, shi ne biki mafi muhimmanci bisa al’adun kasar Sin, wanda ke kara jawo hankalin kasa da kasa. CMG ya hada gwiwa da kamfanin Emaar na Dubai, don gabatar da wasannin kunna fitilu a husumiyar Burj Khalifa, don murnar shiga sabuwar shekarar gargajiya ta kasar Sin. (Murtala Zhang)