logo

HAUSA

Mataimakin shugaban bankin duniya: Tattalin arzikin Sin zai kara bunkasa a bana

2023-01-20 13:06:26 CMG Hausa

Kwanan nan ne, mataimakin shugaban bankin duniya, Axel van Trotsenburg ya zanta da wakilin babban rukunin gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG) a birnin Davos na kasar Switzerland, inda ya bayyana cewa, gudanar da shawarwari tsakanin kasashen Sin da Amurka, da lalibo hanyoyin hadin-gwiwarsu, kyakkyawan albishiri ne ga kasashe masu tasowa, kana, ya yaba da kyautata matakan kandagarkin annobar COVID-19 da kasar Sin ta yi. Yana mai imanin cewa, hakan zai kara samar da ci gaban tattalin arzikin duniya.

Axel van Trotsenburg ya ce, a matsayinsu na manyan kasashe biyu mafiya karfin tattalin arziki a duniya, yin shawarwari na dogon lokaci tsakanin Sin da Amurka, na da matukar muhimmanci ga kamfanonin kasa da kasa, kuma kokarinsu na neman hadin-gwiwa a wasu fannoni, labari ne mai dadi ga kasashe masu tasowa da dama.

Ya kara da cewa, kyautata manufofin dakile yaduwar cutar COVID-19 da gwamnatin Sin ta yi, zai kara samar da makoma mai haske ga karuwar tattalin arzikin kasar da na duniya baki daya. (Murtala Zhang)