logo

HAUSA

Hukumomin cinikayyar Zimbabwe za su shirya taron tattauna bunkasa huldar kasuwanci da kasar Sin

2023-01-20 11:47:28 CMG Hausa

Hukumomin ciniki, da yawon bude ido, da zuba jari na kasar Zimbabwe, sun shirya tsaf, don gudanar da wani taron kasuwanci da nufin bunkasa harkokin kasuwanci da zuba jari da kasar Sin.

Darektan ayyuka a hukumar bunkasa harkokin kasuwancin kasar da ake kira ZimTrade, Similo Nkalata, ya shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua jiya Alhamis cewa, kasar Sin ta zama muhimmiyar abokiyar cinikayya ga kasar Zimbabwe, kuma za a kara kokari wajen inganta dangantakar dake tsakanin kasashen biyu.

Ya ce, ZimTrade tare da hadin gwiwar hukumar zuba jari da raya kasa ta Zimbabwe da hukumar yawon bude ido ta kasar, za su shirya wani taron kasuwanci tsakanin Zimbabwe da Sin, wanda zai mai da hankali kan inganta harkokin kasuwanci, yawon shakatawa da zuba jari a Zimbabwe.

Nkala ya ce, kasar Zimbabwe za ta kara bunkasa harkokin kasuwanci da fadada shigar da kayayyakinta zuwa kasuwanni daban-daban kamar kasashen Sin,da Malaysia, da Masar.

Alal misali, kasar Sin. a matsayinta na mai shigo da kayayyaki da kuma yawan jama'a, wannan kasuwa tana zama daya daga cikin manyan wuraren da Zimbabwe ke fitar da kayayyaki zuwa kasashen waje, inda ta riga ta zama kasa ta uku dake shigo da mafi yawan kayayyakin Zimbabwe cikin kasarta.(Ibrahim)