logo

HAUSA

An wallafa sabon kundin tsarin mulkin jam'iyya cikin harsunan waje

2023-01-19 17:11:15 CMG Hausa

An yi bita tare da amincewa da rahoton da Xi Jinping ya gabatar a babban taron JKS karo na 20 a ranar 16 ga Oktoba, 2022, mai taken “Daga matsayin tutar tsarin gurguzu mai sigar musamman na kasar Sin, da hada kai don gina kasa mai bin tsarin gurguzu ta zamani." da kundin tsarin mulkin jam’iyya, inda babban taron JKS karo na 20 ya amince a wallafa su a cikin harsunan Ingilishi, da Faransanci, Rashanci, da Larabci, Sifaniyanci, da harshen Portuguese, Jamusanci,da Jafananci, da na Bietnam, gami da na Lao da fassara shi daga Sinanci zuwa Turanci, da madaba’ar harsunan waje ta yi. Kuma daga yanzu za a iya samunsu a cikin gida da kuma kasashen waje. (Ibrahim Yaya)