Li Keqiang ya tattauna da masanan ketare dake aiki a Sin gabannin bikin bazara
2023-01-19 10:25:29 CMG Hausa
A yayin da ake shirye-shiryen bikin bazara na gargajiyar kasar Sin, firayin ministan kasar Sin Li Keqiang ya gana da wakilan masanan kasashen ketare wadanda ke aiki a kasar Sin a babban dakin taron jama’a da yammacin jiya, inda ya isar da gaisuwa da fatan alheri ga masanan da iyalansu, da kuma yi musu godiya sakamakon babbar rawar da suka taka kan aikin ingiza cudanya da hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da sauran kasashen duniya. Tare da fatan masanan za su ba da nasu shawarwarin kan yadda gwamnatin kasar Sin take gudanar da ayyukanta.
Yayin tattaunawa ta su, Li Keqiang ya jaddada cewa, kasar Sin za ta nace kan manufar bude kofa ga ketare, da kara habaka kasuwarta ga ketare, da ci gaba da gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninta da sauran kasashen duniya, ta yadda za su dakile kalubalen da suke fuskanta tare, da kuma kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali da wadata a fadin duniya.
Kana Li Keqiang ya yi nuni da cewa, gwamnatin kasar Sin tana maraba ga kwararrun kasa da kasa da su zo kasar su yi aiki, kuma za ta ci gaba da kyautata manufofin hidima da take samarwa musu, ta yadda za a tabbatar da ingancin yanayin rayuwar masanan. (Jamila)