Murnar bikin bazara da shugaba Xi
2023-01-19 14:09:37 CMG Hausa
Bikin bazara, shi ne biki mafi muhimmanci na Sinawa a wannan shekara, inda ake isar da gaisuwa da fatan alheri ga juna.
A duk lokacin da bikin ya gabato, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya kan taya al’ummar kasarsa murnar bikin, inda yake tattaunawa da su domin sauraron matsalolin da suke fuskanta, da burinsu a sabuwar shekara, tare kuma da jin dadin bikin tare da su. (Jamila)