logo

HAUSA

Gina al‘ummar Sin da Afirka mai Koshin lafiya ba batu ne na fatar Baki ba

2023-01-19 22:46:51 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

A bayan garin birnin Addis Ababa na kasar Habasha, akwai jerin wasu gine-gine masu salo na musamman, wadanda suke matukar jan hankalin al’umma, kuma su ne gine-ginen hedkwatar cibiyar kandagarkin cututtuka ta Afirka(Africa CDC) wadanda aka kammala gina su a kwanan baya, wadanda kuma suka mai da cibiyar kandagarkin cututtuka ta Afirka a matsayin daya daga cikin cibiyoyin kandagarkin cututtuka mafiya ci gaba da zamaninta a duniya. Kasar Sin ce ta samar da gudummawar gina shi, matakin da ya sa cibiyar ta zama ta biyu bayan cibiyar taron kungiyar tarayyar Afirka, wadda ita ma kasar Sin ce ta gina.

Afirka nahiya ce da aka fi samun kasashe masu tasowa, inda har yanzu ake fuskantar matsalolin kiwon lafiya, musamman ma sakamakon yaduwar annobar Covid-19, ya zama dole a gaggauta aikin gina tsarin kandagarkin cututtuka ta nahiyar. Yadda aka kammala aikin gina hedkwatar cibiyar kandagarkin cututtuka a Afirka, babu shakka zai inganta karfin kasashen na kandagarkin cututtuka.

Mista Charles Onunaiju, masanin ilmin huldar kasa da kasa na Nijeriya, wanda kuma shi ne darektan cibiyar nazarin harkokin kasar Sin a Nijeriya, yayin da ya tattauna da dan jarida a kwanan baya ya bayyana cewa, “Kasar Sin ta cika alkawarin da ta dauka na fara samar da kasashen Afirka rigakafin cutar Covid-19 da zarar ta kammala nazari da harhada rigakafin, ta kuma sanar da fara aikin gina cibiyar kandagarkin cututtuka ta Afirka kafin lokacin da aka tsai da, ga shi kuma ta kammla aikin yadda ya kamata, kyaun alkawari cikawa, kuma duk wadannan sun shaida kasar Sin kasa ce mai rikon amana. Yanzu kuma ina da imanin cewa, batun gina al‘ummar Sin da Afirka mai Koshin lafiya ba batu ne na fatar Baki ba.”

Daidai kamar yadda mista Onunaiju ya fada, tun bayan bullar cutar Covid-19 a Afirka a shekarar 2020, nan da nan kasar Sin ta samar da gudummawarta, kuma shugaban kasar Sin Xi Jinping ya shugabanci taron hadin kan Sin da Afirka kan yaki da cutar Covid-19, inda ya gabatar da manufar nan ta gina al‘ummar Sin da Afirka mai koshin lafiya, kuma kawo yanzu, kasar Sin ta samar da rigakafi sama da miliyan 189 ga kasashen Afirka sama da 50, baya ga yadda ta yi kokarin aiwatar da hadin gwiwa da Masar da dai sauran kasashen Afirka, don kasashen su samu kwarewar samar da rigakafin da kansu. Ban da wannan, kasar Sin ta kuma tura tawagogin masana ilmin kiwon lafiya 5 da kuma kungiyoyin ma’aikatan lafiya 46 zuwa kasashen Afirka don su ba da taimako wajen dakile cutar a Afirka. Ga shi yanzu, kasar Sin ta kammala aikin gina hedkwatar cibiyar kandagarkin cututtuka ta Afirka tare da mika ta hannun kungiyar tarayyar Afirka.

Daga wannan sabon mafari, muna fatan za a kara cimma sabbin ci gaba ta fannin ayyukan kiwon lafiya a kasashen Afirka bisa ga manufar nan ta gina al‘ummar Sin da Afirka mai koshin lafiya, don ta kasance laimar da ke kare al’ummomin kasashen Afirka daga cututtuka.(Mai Zane:Mustapha Bulama)