logo

HAUSA

Liu He ya tattauna da sakatariyar baitulmalin Amurka

2023-01-19 10:40:11 CMG Hausa

A yammacin jiya ne, mataimakin firayin ministan kasar Sin kuma  jagoran tawagar kasar Sin kan tattaunawar tattalin arziki tsakanin Sin da Amurka Liu He ya tattauna da sakatariyar baitulmalin Amurka Janet Yellen a birnin Zurich na kasar Switzerland.

Yayin tattaunawar ta su, sassan biyu sun yi imanin cewa, ana kokarin farfado da tattalin arzikin duniya a halin yanzu, don haka ya dace kasashen Sin da Amurka su kara karfafa tattaunawa da daidaita manufofin tattalin arziki, domin dakile kalubalen tattalin arziki da hada-hadar kudi tare, lamarin da zai amfanawa kasashen biyu, gami da duniya baki daya. Sassan biyu sun kuma amince za su kara karfafa hadin gwiwa tsakaninsu, karkashin tsare-tsaren bangarori biyu da MDD da G20 da APEC da sauransu. Haka kuma, za su ci gaba da goyon bayan sauyin tsarin tattalin arziki da bunkasuwar kasashe masu tasowa ba tare da gurbata muhalli ba. Ban da haka, bangaren kasar Sin ya nuna damuwa kan manufofin tattalin arziki da cinikayya da fasaha da Amurka ke aiwatarwa kan Sin, kuma yana fatan bangaren Amurka zai mai da hankali kan tasirin manufofin ga kasashen biyu.

Haka zalika kasar Sin ta yi maraba da Yellen da ta kawo ziyara kasar Sin a lokacin da ya dace a bana. Haka kuma sassan biyu sun amince cewa, tawagogin dake tattauna batutuwan tattalin arziki da cinikayyar, za su ci gaba da yin cudanya a matakai daban daban. (Jamila)