logo

HAUSA

Mutane 16 ne sun mutu a hatsarin jirgin sama mai saukar ungulu a kusa da Kiev na Ukraine

2023-01-19 12:36:45 CMG Hausa

Wani jirgin sama mai saukar ungulu ya yi hatsari a kusa da birnin Kiev, inda mutane 16 suka mutu, ciki har da ministan harkokin cikin gida na Ukraine Denys Monastyrsky.

Hukumar ba da agajin gaggawa ta Ukraine ta ce, hatsarin da ya afku a garin Brovary da ke wajen birnin Kiev, ya kuma yi sanadiyar mutuwar mataimakin Monastyrsky, Mr Yevhen Yenin, yayin da wasu 30 kuma suka jikkata.

Tun da farko, jami'ai sun ba da adadin mutuwar mutane 18. Monastyrsky, da Yenin, da sakataren ma'aikatar harkokin cikin gidan Ukraine Yuriy Lubkovych, da wasu mutane shida na cikin jirgin da ya fadi. (Ibrahim Yaya)