logo

HAUSA

Me Sin Ta Kawo wa Duniya Cikin Shekaru 3 Da Ta Shafe Tana Kokarin Tinkarar Cutar COVID-19

2023-01-19 22:20:38 CMG Hausa

Yau Alhamis, 19 ga wannan wata, ita ce kwana ta 11 da aka mayar da cutar COVID-19 zuwa rukunin B a kasar Sin. Bisa bayanin da hukumar kiwon lafiya ta kasar ta yi, an ce, yawan mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 mai tsanani ya fara raguwa a larduna daban daban na kasar Sin. Yanzu haka Sinawa suna maraba da zuwan bikin Baraza cikin koshin lafiya. An kuma samu wannan yanayi ne domin Sin ta dauki matakan yaki da cutar COVID-19 yadda ya kamata, wadanda suka samar da manyan nasarori a kasar.  

A cikin shekaru 3 da suka gabata, gwamnatin kasar Sin ta yi kokarin tabbatar da lafiyar dukkan jama’arta. Sin ta yi ta gabatar da kididdiga da bayanai game da cutar ga kasa da kasa, don samar da gudummawa wajen yaki da cutar, da nazarin alluran rigakafin cutar, da kuma kayayyakin gwajinta. 

Game da tattalin arziki kuwa, Sin ta raya tattalin arziki da zamantakewar al’umma yayin da take tinkarar cutar ta COVID-19, wadda ta kasance kasa dake kan gaba wajen farfardo da tattalin arzikin duniya. A cikin shekarun 3, yayin da ake tinkarar yaduwar cutar, da ra’ayoyin bangare daya da ba da kariya ga bangare daya da kuma cinikayya, Sin ta kara bude kofa ga kasashen waje, hakan ya tabbatar da samar da kayayyaki a duniya yadda ya kamata.

A halin yanzu, ba a ga bayan cutar COVID-19 a duniya ba, ya kamata kasa da kasa su yi kokari tare don tinkarar kalubalen. Kasar Sin mai samun farfadowa za ta sa kaimi ga hadin gwiwa a tsakanin kasa da kasa wajen yaki da cutar da kuma samar da gudummawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya baki daya. (Zainab)