logo

HAUSA

Zargin “Tarkon Bashi” Ba Zai Katse Alakar Sin Da Kasashen Afirka Ba

2023-01-19 18:11:51 CMG Hausa

Sau da yawa mun sha jin yadda wasu kasashen yammacin duniya, da kafofin watsa labaransu na furta kalamai na zargi, cewa wai kasar Sin tana danawa kasashen dake nahiyar Afirka “Tarko Bashi”, karkashin manufofinta na cudanyar da kasashe masu tasowa.

Irin wadannan sassan, kan Ambato shawarar ziri daya da hanya daya, a matsayin shiri dake dorawa kasashen na Afirka tarin bashi da ba za su iya biya ba. To amma abun tambayar shi ne, ko kasashen na Afirka suna da irin wannan tunani?

A zahiri dai, ba wata kafa da ta taba fito da shaidu, ko kafa sahihan dalilai kan wancan zargi da wasu kasashen yamma ke yiwa kasar Sin. Hasali ma, sau da yawa mun sha jin shugabannin kasashen Afirka na godewa irin tallafi, da gudummawar da Sin din ke ba su, a kokarinsu na raya kasa da samun ci gaba mai dorewa.

Ko da a yayin ziyarar aiki da ministan harkokin wajen kasar Sin Qing Gang ya kai kasashen Afirka 5, da helkwatar AU, da kungiyar tarayyar Larabawa a baya bayan nan, mun ga irin yadda bangarorin da ya zanta da su suka rika nuna gamsuwa, da godiya kan manufofin kasar Sin, na tafiya tare da kawayenta na Afirka, a matsayinsu na aminai, kuma ’yan uwan ta kasashe masu tasowa.

Kaza lika, masana tattalin arziki da dama na bayyana cewa, bashin da gwamnatoci ke karba daga waje, ba ya haifar da koma bayan tattalin arziki, muddin an aiwatar da sharudda, da matakan cin gajiyarsa yadda ya kamata. Kuma karkashin hakan ne ragowar cibiyoyin bayar da lamuni na yammacin duniya, suke baiwa kasashen na Afirka lamuni mai kudin ruwa, tare da gindaya sharudda gare su na biyan basussukan. Sabanin haka, kasar Sin a nata bangare, ba ta gindaya sharudda ga kasashen da take baiwa bashi, kuma bashin Sin yana da rangwame matuka, idan an kwatanta da na sauran cibiyoyin ba da lamuni na kasa da kasa.

Idan kuma muka komawa misalai daga su kansu jagororin kasashen Afirka, da kuma alkaluman da hukumomin nahiyar ke fitarwa, game da tasirin lamunin kasar Sin a nahiyar Afirka, za mu ga a kasashe irin su Najeriya, da Zambia, da Kenya da Angola da sauransu, ayyukan more rayuwa da kasar Sin ta tallafawa wajen samarwa, suna zamewa kasashen abubuwan alfahari.

Duba da haka, masharhanta da dama ke cewa, su kansu kasashen yamma, da masana na kasashen yammacin duniya, sun gamsu da kyakkyawan tasirin alakar Sin da kasashen Afirka, da ma yadda Sin din ke samar da tallafi ga ci gaban tattalin arziki da zamantakewar al’ummun nahiyar. Amma duk da haka, wasu bangarori na kitsa karairayi, domin bata wannan kyakkyawar alaka, ta fakewa ba batun "Tarkon bashi ". Suna kuma yada kalamai marasa hujja, da nufin siyasantar da alakar dake tsakanin sassan biyu.

Sai dai duk da haka, alamu na zahiri sun tabbatar da cewa, Sin da kasashen Afirka sun amince da juna, kuma ba wani rukuni, ko wasu masu kitsa karairayi da za su iya yin nasarar bata wannan kyakkyawar alakar da sassan biyu suka gina cikin tsawon lokaci. (Saminu Hassan)