logo

HAUSA

Aiwatar da yerjejeniyar AfCFTA za ta bunkasa kasuwanci tsakanin kasashen Afirka

2023-01-19 11:06:48 CMG Hausa

Mukaddashin babban sakataren hukumar MDD mai kula da tattalin arzikin Afirka (UNECA) Antonio Pedro, ya bayyana cewa, ya kamata a gaggauta aiwatar da yarjejeniyar yankin ciniki cikin 'yanci na Afirka (AfCFTA), domin yankin zai bunkasa harkokin kasuwanci tsakanin Afirka tare da habaka masana'antu. 

Wata sanarwar da hukumar ta UNECA ta fitar, ta ruwaito Pedro na cewa, duba da tarin alheran dake kunshe cikin yarjejeniyar, a hannu guda kuma, za su iya tabbata ne kawai, idan aka aiwatar da yarjejeniyar yadda ya kamata.

Pedro ya ce, babban burin yarjejeniyar shi ne, taimaka wa kasashe masu karancin ci gaba murmurewa da kara bunkasa. Yana mai ba da misali da kiyasin da UNECA ta yi na baya-bayan nan, wanda ya nuna cewa, muddin aka aiwatar da yarjejeniyar cikin nasara, babu makawa zai yi tasiri sosai ga GDP, da kasuwanci da ma walwalar jama’ar nahiyar.

Pedro ya ce, nasarar aiwatar da yarjejeniyar ta AfCFTA, za ta taimaka wajen kara karfin Afirka da kuma yiwuwar rage dogaron kasuwancin da take yi a halin yanzu kan abokan huldar kasashen waje.

A cewarsa, wannan ya kasance mai mahimmanci bisa la’akari da raunin nahiyar da ya fito fili sakamakon cutar ta COVID-19, da rikicin Ukraine. Ya kara da cewa, Afirka na bukatar rage illar da ke tattare da abubuwa marasa kyau da za su iya kunno kai a nan gaba. (Ibrahim Yaya)