logo

HAUSA

Ruwan Da ya Buge Ka...

2023-01-18 17:47:51 CMG Hausa

A wannan makon ne sabon ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, ya kammala ziyarar da ya kai kasashen Habasha da Angola da Gabon da Benin da Masar, ziyarar dake zama ta farko ga ministan tun bayan nada shi kan wannan mukami. Kana ta 33 cikin jerin ziyarar da ministocin harkokin wajen kasar Sin ke kaiwa wasu kasashe nahiyar a duk farkon kowa ce shekara.

Wannan mataki ya kara nuna muhimmancin da kasar Sin ta dora kan alakarta da nahiyar Afirka, da ma kasashe masu tasowa, da kara jaddada kudurin kasar Sin na samun ci gaba tare gami da kyakkyawar makoma.

Sabanin yadda wasu kasashen yamma ke nuna cewa, suna tare da kasashen Afirka, amma ba tare da ganin shaidar hakan a zahiri ba. A nata bangare, kasar Sin ta kara tabbatar da cewa, ita sahihiyar kawa ce kuma abokiyar hadin gwiwar nahiyar Afirka, bisa ga sahihan manufofi da irin sakamako na zahiri da imanin da take nunawa. Bugu da kari, kasar Sin tana mutunta zabin al'ummar Afirka na bin hanyar ci gaban da ta dace da yanayinsu, haka kuma ba ta taba tilasta musu yin wani abu ko gindaya musu wani sharadi ba. Gani da ido aka ce maganin tambaya.

Masharhanta sun sha bayyana cewa, nahiyar Afirka wani babban dandali ne na hadin gwiwa tsakanin kasashen duniya, amma ba fagen adawa da manyan kasashen duniya ba. Haka kuma nahiyar Afirka, nahiya ce mai tasowa, mai cike da arziki da fata da kuma kuzari. Don haka, idan ba a samu zaman lafiya da ci gaba a Afirka ba, to, ba za a samu kwanciyar hankali da wadata a duniya ba. Kuma wannan ya dace da ra’ayin kasar Sin.

Abin da Afirka ke bukata, shi ne goyon baya da hadin kai, ba nuna adawa ba. Sanin kowa ne cewa, babu wata kasa ko wasu daidaikun mutane dake da ikon tilastawa kasashen Afirka karkata ga wani bangare.  Haka kuma babu wanda zai iya raba alakar Sin da Afirka. Domin ruwan da ya buge ka shi ne ruwa.(Ibrahim Yaya)