logo

HAUSA

Kuduri game da gudanar da taro na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin karo na 14

2023-01-18 16:05:33 CMG Hausa

Taro karo na 25, wanda zaunanen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin karo na 13 ya gudanar, ya zartas da kuduri game da gudanar da taro na farko, na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin karo na 14.

Taron ya yanke kuduri cewa, za a gudanar da taro na farko na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin karo na 14, a ranar 4 ga watan Maris na shekarar 2023 a birnin Beijing.

Kaza lika babbar ajandar taron ta hada da duba rahoton ayyuka, da rahoton ba da shawara wanda zaunannen kwamitin majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa na kasar Sin ya gabatar, da dubawa, da zartas da dokokin da aka kyautata na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin, da zabar shugaba, da mataimakin shugaba, da babban sakatare, da kuma mambobin zaunanen kwamitin na majalisar ba da shawara kan harkokin siyasa ta kasar Sin karo na 14, da halartar taron farko na majalisar wakilan jama'ar kasar Sin karo na 14, da saurare, tare da tattauna rahoton aikin gwamnati, da sauran rahotannin. (Safiyah Ma)