logo

HAUSA

Ziyarar Qin Gang a Afirka ta kawo wa hadin gwiwar Sin da Afirka sakamakon gani maimakon cika alwashi kawai

2023-01-18 09:08:56 CMG Hausa

Kamar yadda aka saba, a farkon kowace sabuwar shekara, ministan harkokin wajen kasar Sin kan ziyarci wasu kasashe a nahiyar Afrika. A bana ma, sabon ministan harkokin wajen Sin Qin Gang, ya ziyarci kasashen Afrika da suka hada da Habasha da Gabon da Angola da Benin da Masar, da kuma hedkwatocin AU da AL, wadda kuma ita ce ziyararsa ta farko a ketare bayan nada shi kan wannan mukamin.

Wannan ziyara dai wata dadaddiyar al'ada ce dake zama ta tsawon shekaru 33 a jere da kowane ministan harkokin wajen kasar Sin ke fara kai ziyara kasashen Afirka a farkon kowace sabuwar shekara.

Wannan mataki ya kara nuna muhimmancin da kasar Sin ta dora kan alakarta da nahiyar Afirka, da ma kasashe masu tasowa. Haka kuma matakin ya kara jaddada kudurin kasar Sin na samun ci gaba tare gami da kyakkyawar makoma.

A yayin rangadin da ya kai shi kasashen nahiyar biyar, Qin Gang, ya tattauna da shugabannin Afirka kan yadda za a aiwatar da matakan da aka tsara a taron kolin dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka (FOCAC) .

Kasar Sin ta kara tabbatar da cewa, ita sahihiyar kawa ce kuma abokiyar hadin gwiwar nahiyar Afirka, bisa ga sahihan manufofi da irin sakamako na zahiri da imanin da take nunawa. Bugu da kari, kasar Sin tana mutunta zabin al'ummar Afirka na bin hanyar ci gaban da ta dace da yanayinsu, haka kuma ba ta taba tilasta musu yin wani abu ko gindaya musu wani sharadi ba. 

Kana idan suka fuskanci wani kalubale ko matsaloli, kasar Sin ta kan nemi hanyar ba su taimako ta hanyar da ta dace ta hanyar tattaunawa da abokan huldar ta Afirka. A shirye kasar Sin take ta taimakawa Afirka, a lokacin da bukatar hakan ta taso. Cikin gomman shekaru ke nan a jere, kasar Sin tana tura tawagogin ma'aikatan lafiya zuwa kasashen Afirka domin yakar cututtuka, baya ga masana aikin gona da samar da taimakon kudi da kwarewa da take bayarwa domin farfado da ababan more rayuwa da kawar da talauci. (Saminu,Ibrahim/Sanusi Chen)