logo

HAUSA

MDD ta yi kira da a gaggauta sakin matan da aka yi garkuwa da su a Burkina Faso

2023-01-18 10:26:08 CMG Hausa

MDD ta yi kira da a dauki matakan gaggauta sakin mata da ’yan matan nan su kimanin 50, da aka yi garkuwa da su a ranaikun Alhamis da Juma’ar makon jiya, lokacin da suke kokarin samo kayan lambu daga wasu dazuka dake kusa da wasu kauyuka 2, kusa da garin Arbinda dake arewacin kasar Burkina Faso.

Rahotanni sun tabbatar da cewa, wasu gungun ’yan bindiga dauke da makamai ne suka sace matan, da ba su ji ba su gani ba.

Game da hakan, babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya yi Allah wadai da aukuwar lamarin, yana mai kira ga hukumomi a Burkina Faso, da su yi duk mai yiwuwa wajen ceto matan da aka sace, tare da gurfanar da wadanda suka aikata wannan ta’asa gaban shari’a.

Bugu da kari, Mr. Guterres ya kuma alkawarta ci gaba da aiki tare da kasashen yammacin Afirka, da sauran abokan hulda, ciki har da inganta matakan kare fararen hula, da tallafawa duk wani kokari na wanzar da zaman lafiya. Ya ce kasashen yankin yammacin Afirka da Sahel, na ci gaba da fuskantar kalubale da dama, ciki har da mummunan yanayin tsaro.

A nata bangare, shugabar ofishin MDDr na shiyyar yammacin Afirka ko UNOWAS Giovanie Biha, ta ce ayyukan masu dauke da makamai, da masu tsattsauran ra’ayi, da masu aikata miyagun laifuka sun tursasa rufe dubban makarantu, da cibiyoyin kula da lafiya, tare da raba miliyoyin al’umma da gidajen su a yankin.  (Saminu Alhassan)