logo

HAUSA

Firaministan Sin ya jaddada muhimmancin daidaita samarwa da cinikin makamashi domin inganta rayuwar al’umma

2023-01-18 12:03:33 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya jaddada muhimmancin daidaita samar da makamashi, da inganta farashin sa, domin kyautata tattalin arziki, da bunkasa zamantakewar al’umma.

Li Keqiang, ya yi tsokacin ne yayin zayarar gani da ido da ya kai babban kamfanin lantarki na Sin a jiya Talata. Bayan sauraron rahoto game da makamashin da ake samarwa a kasar, Li ya ce yayin da ake fuskantar yanayi mai sarkakiya a gida da waje, a bara kasar Sin ta aiwatar da matakai daban daban, domin rage wahalhalun da kamfanoni ke fuskanta a sana’oin samar da lantarki ta kwal, tare da ba da tabbaci ga samar da isasshen makamashi a gidaje, da tallafawa ci gaban tattalin arziki bakin gwargwado, da biyan bukatun al’umma na yau da kullum.

Ya ce duk da hauhawar farashin kayayyaki da ake fuskanta a duniya baki daya, farashin hajoji a Sin ya karu ne da kaso 1.8 bisa dari kacal a watan Disamba, sakamakon daidaiton da ake da shi a fannin samar da makamashi a cikin gida.  (Saminu Alhassan)