logo

HAUSA

Akwai yiwuwar jami’an shige da ficen kasar Saudiya su fara aikin tantance alhazan Najeriya daga gida

2023-01-18 09:40:09 CMG Hausa

A ranar 17 ga wata ma’aikatar lura da harkokin aikin hajji ta kasar Saudiya ta tabbatar da cewa za ta fara nazari a kan bukatar Najeriya na neman jami’an shige da fice kasar su rinka aikinsu na tantance alhazan tarayyar Najeriya daga gida maimakon a birnin Jedda.

A lokacin da yake karbar bakuncin wakilan hukumar aikin hajji ta Najeriya, mataimakin babban jami’in ma’aikatar Umar Abashi ya ce, kasar Saudiya ta jima da bullo da wannan tsari na tantance alhazai daga kasashensu, inda ta fara aikin gwaji da kasashen Malasiya da Indonisia.

Kamar yadda ya ce an sami sakamako mai kyau a ’yan shekarun da aka shafe ana yi, a don haka ma’aikatar za ta yi kokarin ganin an saka Najeriya cikin tsarin kamar yadda shugaban hukumar aikin Hajji ta Najeriya Alhaji Zikrullah Kunle Hassan ya nema.

A yayin ziyarar, shugaban hukumar alhazai ta Najeriya ya yaba bisa yadda kasar ta Saudiya ta sake baiwa Najeriya adadin kujeru dubu 95 a aikin hajjin dake tafe, sai dai ya sake neman mahukuntan na Saudiya su rinka barin kaso 80 na alhazan Najeriya su rinka ziyartar Madina kafin hawan arfa. (Garba Abdullahi Bagwai)