Liu He ya halarci taron shekarar shekara na dandalin tattalin arzikin duniya na 2023
2023-01-18 16:00:23 CMG Hausa
Mataimakin firayin ministan majalisar gudanarwar kasar Sin Liu He, ya halarci taron shekarar shekara na dandalin tattalin arzikin duniya na Davos na shekarar 2023, tare da gabatar da jawabi.
Cikin jawabin na sa, Liu He ya ce bisa ruhin babban taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20, tsayawa tsayin daka kan bunkasuwa, shi ne aiki mafi muhimmanci cikin ayyukan raya tattalin arzikin Sin na 2023, kuma da tsayawa tsayin daka kan hanyar yin gyare-gyare ga fannin tattalin arziki irin na kasuwanci na gurguzu, da tsayawa tsayin daka kan habaka bude kofa ga kasashen waje a dukkan fannoni, da kuma tsayawa tsayin daka kan kirkire-kirkire don samun ci gaba.
Ya ce bisa kokarin da aka yi, tattalin arzikin Sin na bana zai samu kyautatuwa daga duk fannoni.
Liu He ya ce, bisa yanayin kasar Sin, dole ne kasar ta bude kofa ga kasashen waje, ta ci gaba da kara daga matsayin bude kofa, kuma ta nuna adawa ga ra’ayin bangaranci, da ba da kariyar cinikayya, kana za ta inganta karfafa hadin gwiwar kasa da kasa a dukkan fannoni.
Yayin taron, Liu He ya kuma gana da wasu manyan jami’ai, da masana, da 'yan kasuwa na kasashen da batun ya shafa bisa gayyata. (Safiyah Ma)