logo

HAUSA

Ana ci gaba da bincike domin ceto mata kimanin 50 da ’yan bindiga suke sace a Burkina Faso

2023-01-17 11:23:10 CMG Hausa

Gwamnan lardin Soum na kasar Burkina Faso, Laftana kanal Rodolphe Sorgho ya ce, jami’an tsaro na ci gaba da farautar ’yan bindigar da suka yi awon gaba da wasu mata da yaransu kanana su kimanin 50, daga wasu kauyukan yankin 2.

Mr. Sorgho, wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwar da ya fitar a jiya Litinin ya ce, rahotanni sun tabbatar da cewa, a daren ranaikun Alhamis da Juma’ar makon jiya, wasu mahara dauke da makamai sun sace gungun wasu mata, da yaransu kimanin su 50, daga kauyukan Liki, da wani kauyen dake yammacin Aribinda.

An ce matan sun shiga dazukan dake kusa da kauyukan su ne domin tsinko kayan marmari, lokacin da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su.

To sai dai jim kadan da samun labarin aukuwar lamarin, a cewar gwamna Sorgho, jami’an tsaro sun bazama domin ceto matan da yaransu kanana, da kuma cafke ’yan bindigar da suka aikata wannan ta’asa. (Saminu Alhassan)