logo

HAUSA

Kasar Sin Na Samun Bunkasuwa Mafi Girma A Duniya

2023-01-17 22:03:21 CMG HAUSA

Hukumar kididdiga ta kasar Sin ta gabatar da bayanan tattalin arzikin kasar a shekarar 2022, wanda ya nuna cewa, a shekarar 2022 jimillar GDP a kasar Sin ta kai kudin Sin RMB yuan biliyan 121020.7, wadda ta karu da 3.0% kan ta shekarar 2021. GDPn kasar Sin ta sake kafa tarihi, ta wuce yuan triliyan 120, bayan da adadin ya wuce yuan triliyan 100 a shekarar 2020, kana yuan triliyan 110 a shekarar 2021.

Ko da yake kasar Sin ta fuskanci matsalar rashin kwanciyar hankali a harkokin siyasa a wasu sassan duniya, karuwar barazanar koma bayan tattalin arzikin duniya, yaduwar annobar cutar COVID-19 a gida, da sauran batutuwan ba zata da suka wuce zaton mutane, ta daidaita matsin lamba yadda ya kamata, GDPn ta ya sake kafa tarihi, lamarin da yake da matukar wuya. Asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ya yi hasashen cewa, karuwar GDP a kasashen Amurka da Japan a shekarar 2022 ba za ta wuce 2% ba. Kana a duk fadin duniya, karuwar GDPn kasar Sin da 3% a shekarar 2022, ta fi yawancin manyan rukunonin tattalin arziki, lamarin da ya nuna cewa, kasar Sin tana da juriya da kuzari.

Yanzu kasar Sin tana fito da karin kuzari kan raya tattalin arziki saboda ta shiga sabon mataki na yaki da annobar COVID-19. Yawan zirga-zirgar jiragen sama a gida ya kai 80% ko fiye da haka bisa na shekarar 2019. A sabuwar shekarar da ake ciki, kasar Sin na da karfin gwiwa kan farfadowar tattalin arzikinta sakamakon kayayyaki masu dimbin yawa da take da su, kasuwanni a gida, zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga ketare, da kyawawan fasahohin daidaita harkokin tattalin arziki daga manyan tsare-tsare. (Tasallah Yuan)