logo

HAUSA

Lawal Saleh: Ziyarar ministan harkokin wajen kasar Sin a Afirka za ta ci gaba da sada zumunta tsakanin bangarorin biyu

2023-01-17 14:53:52 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Qin Gang, ya ziyarci kasashen Habasha, da Gabon, da Angola, da Benin, da Masar, da kuma helkwatar kungiyar tarayyar Afirka AU, da helkwatar kungiyar kasashen Larabawa, tsakanin ranakun 9 zuwa 16 ga watan Janairun bana. Wannan ita ce ziyara ta farko da Qin Gang ya kai kasashen ketare, tun bayan kama aiki a matsayin ministan harkokin wajen kasar ta Sin. Kaza lika bana ce shekara ta 33 a jere, da ministan harkokin wajen Sin ke kai ziyarar aiki ta farko a duk shekara, zuwa kasashen Afirka.

Wakilin mu Murtala Zhang ya tattauna da shahararren mai sharhi kan al’amuran yau da kullum dake Abuja, fadar mulkin tarayyar Najeriya, Malam Lawal Saleh, don jin ta bakin sa kan muhimmancin ziyarar minista Qin Gang a wannan karo, gami da fatan sa ga makomar dangantakar kasar Sin da kasashen Afirka a shekara ta 2023. (Murtala Zhang)