logo

HAUSA

Shirin Spring Bud ya taimaka wa ‘yan matan yankin Liangshan na Sin wajen yaki da talauci da jahilci da fara sabuwar rayuwa

2023-01-17 08:30:05 CMG Hausa


A ranar 11 ga watan Oktoban 2021, ranar 'ya'ya mata ta duniya karo na 10. Madam Peng Liyuan, manzon musamman ta Shirin Spring Bud, mai rajin inganta ilimin 'ya'ya mata a kasar Sin, ta sanar da kaddamar da shirin Dream of the Future Action, domin yayatawa da aiwatar da shirin wanda ke karkashin Shirin Spring Bud. A ranar 7 ga watan Junairun 2022, asusun kula da kananan yara da matasa 'yan kasa da shekaru 20 na kasar Sin (CCTF), ya kaddamar da wani shirin raya ilimin 'ya'ya mata a yankin Liangshan, a makarantar midil ta Xining dake yankin Liangshan na kabilar Yi mai cin gashin kansa dake lardin Sichuan na kudu maso yammacin kasar Sin, inda aka bayar da gudunmuwar kudi da kayayyakin da darajarsu ta kai yuan miliyan 48, kwatankwacin dala miliyan 7.06, domin taimakawa 'yan matan Liangshan. A matsayin wani muhimmin bangare na shirin Spring Bud, shirin Dream of Future Action, zai ci gaba da tallafawa ilimin 'ya'ya mata da dukkan ayyukan raya yankin Liangshan.

Liangshan, inda tsaunin Daliangshan yake, mazauni ne mafi girma na 'yan kabilar Yi a kasar Sin. akwai mazauna miliyan 4.86, inda fiye da rabinsu suka kasance 'yan kabilar Yi.

A baya, 1 bisa 4 na 'yan matan da suka kai matakin shiga makaranta ne kadai suke karatun firamare, kuma kalilan daga cikinsu ne ke kammala makarantar firamare. Adadi mai yawa na 'yan matan ne ke barin makaranta.

A 1992, da taimakon Margaret Chow Kit Bing daga yankin Hong Kong na Sin, asusun CCTF ya kaddamar da ajujuwan 'yan mata karkashin shirin Spring Bud, a gundumar Butuo ta Liangshan, domin taimakawa 'yan matan kabilun Yi da Miao da sauran wasu kabilun da suka bar makaranta, sake komawa aji.

Tun bayan kaddamar da shi da asusun CCTF ya yi a 1989, Shirin Spring Bud, ya samar da gudunmuwar sama da yuan biliyan 2 da miliyan 586, kwatankwacin dala miliyan 380, kuma an yi amfani da kudin ne wajen taimakawa ‘yan mata sama da miliyan 3.96 samun ilimi da cimma burikansu, cikinsu har da wadanda suke Liangshan.

Wang Fuxiu, 'yar asalin kabilar Miao ce dake cikin tsaunin Daliangshan. Ta bar karatu bayan ta kammala makarantar firamare. A 1992, ta koma makaranta da taimakon Shirin Spring Bud.

A shekarar 1993, ita da wasu dalibai da aka zaba a matsayin dalibai masu hazaka na Shirin, suka taho Beijing domin ziyarar da asusun CCTF ya shirya. Sun gudanar da shirye-shirye da dama, kuma sun ziyarci wurare da dama a birnin. Ziyarar ta bude idanun Wang Fuxiu.

Bayan ta kammala karatun Sakandare, ta ci jarrabawar neman aikin gwamnati. Ta nemi aiki a Sike, daya daga cikin garuruwa mafi koma baya a gundumar. Ta kan ja hankalin mazauna kauyen game da muhimmancin ilmantar da 'ya'yansu. Shekaru biyu bayan nan, ta zama shugabar kungiyar mata ta garin Le'an. 

A shekarar 2005, ta fara aiki a ofishin kula da hada-hadar kudi na Xixihe. A 2014 kuma, aka sauya mata wajen aiki zuwa wani sashe na reshen JKS a gundumar Butuo. A shekarar 2016, aka dora mata alhakin jagorantar aikin yaki da talauci a Yonggedeng. Ta karfafawa mutanen kauyen gwiwar kiwon lafiyarsu da shirya gini ban dakuna da wuraren wanka a kauyen. kuma bisa jagorancinta, mutanen kauyen suka fara shuka nau’in shinkafa na water oats a 2019, kuma ya taimaka musu samun karin kudin shiga. Ta ce za ta jagoranci mata wajen fara kasuwancinsu na kansu a nan gaba.

A ranar 17 ga watan Nuwamban 2020, aka cire gundumomi 7 na karshe dake Liangshan, daga jerin yankuna masu fama da talauci. Al'ummar dukkan kabilu a Liangshan, da al'ummar baki dayan kasar Sin, sun samu ci gaba da kyautatuwar zamantakewa ta ko wace fuska, kuma suna ci gaba da samun ci gaba, yayin da ake kokarin cimma burin cika shekaru 100 da kafuwar Jamhuriyar jama'ar kasar Sin, wanda shi ne gina kasar Sin ta zamani mai bin tsarin gurguzu da demokradiyya, mai karfi da ci gaban al'adu da kyan muhalli da zaman lafiya.

Shirin Spring Bud, dake mayar da hankali kan yaki da talauci ta hanyar samar da ilimi, da kuma tabbatar da daidaiton jinsi a fannin ilimi, ya shafe shekaru 30 yana aiki a Liangshan. Shirin ya zama wani muhimmin karfi da al'ummar kabilar Yi da sauran kabilu ke amfani da shi wajen yaki da talauci da jahilci da kuma fara sabuwar rayuwa ta samun ci gaba.

A watan Junairun shekarar 2022, bayan shirin da aka shafe watanni 3 ana yi, aka kaddamar da shirin raya ilimin 'ya'ya mata a Liangshan na asusun CCTF a birnin Xichang. Baya ga ilimi, shirin yana kuma inganta farfado da kauyuka da taimakawa wajen karfafa nasarorin da aka cimma a bangaren yaki da talauci.

Zhu Xisheng, mataimakin shugaban asusun CCTF na wancan lokaci, ya ce asusun zai taka rawa a matsayinsa na mai inganta walwalar al'umma, wajen cimma ci gaba na bai daya ta hanyar tsarin nan, na manyan kamfanoni su taimakawa al'umma, ciki har da bayar da kyaututtuka da gudunmuwar jin kai. Kuma asusun zai bude wani sabon babi na kokarin cimma burin cika shekaru 100 da kafuwar jamhuriyar jama'ar kasar Sin, tare da al’ummar dukkan kabilu dake Liangshan.(Kande Gao)