logo

HAUSA

Ba zai yiwu a shafawa amfanin allurar rigakafin Sin bakin fenti ta hanyar kitsa karya ba

2023-01-17 11:13:17 CMG Hausa

A halin yanzu, kasar Sin tana kyautata manufofinta na kandagarkin annobar cutar COVID-19, matakin da ya samu maraba daga dukkanin sassan duniya. Amma wasu ‘yan siyasa, da kafofin watsa labarai na kasar Amurka, suna sake shafawa alluran rigakafin cutar da kasar Sin ta samar bakin fenti, kuma yunkurinsu shi ne musunta kokarin da kasar Sin take yi kan aikin dakile yaduwar cutar, tare kuma da sayar da karin magungunan kamfanonin kasar a kasar Sin.

Kawo yanzu, adadin nau’ikan rigakafin kasar Sin ya riga ya kai 13, wadanda ake samarwa daga fasahohi iri 4. Kaza lika nazarin kimiyya, da sakamakon rigakafin da aka samu sun nuna cewa, allurar rigakafin kasar Sin sun dace da ma’aunin hukumar kiwon lafiyar duniya WHO, wato suna magance kamuwa da cutar, da magance kamu da nau’ikan ta masu tsanani, da kuma magance mutuwa sakamakon kamuwa da cutar.

Bugu da kari, sakamakon gwajin shi ma ya nuna cewa, rigakafin kasar Sin yana da inganci da tsaro, kuma tuni an riga an yi alluran ga Sinawa da yawan su ya kai kaso 92.9 bisa dari. Ciki Sinawan har da tsofaffi wadanda shekarunsu suka kai sama da 60 da yawan su ya kai kaso 90 bisa dari. Ban da haka, kasar Sin ta shiga shirin COVAX, inda ta samar da rigakafi biliyan 2.2 ga kasashen duniya sama da 120.

Allurar rigakafin COVID-19, makami ne na shawo kan cutar, ba makamin siyasa da ake amfani da shi domin shafawa sauran kasashe bakin fenti ba, don haka ya dace irin wadannan ‘yan siyasar Amurka, su cika alkawarin da suka yi, na samar da rigakafi kyauta ga masu bukata, ta yadda za su taka rawar da suke iyawa, a aikin kandagarkin cutar a kasar su, da ma a fadin duniya baki daya. (Jamila)