Ya kamata Amurka ta sanar da bayanai da alkaluma kan cutar COVID-19
2023-01-17 20:31:58 CMG Hausa
Kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin ya bayyana a gun taron manema labaru da aka gudanar a yau Talata cewa, ya kamata kasar Amurka ta sanar da bayanai da alkaluma kan annobar cutar COVID-19 tare da hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO da gamayyar kasashen duniya cikin lokaci ba tare da rufa-rufa ba, da daukar matakai don hana yaduwar cutar.
Wang Wenbin ya yi nuni da cewa, a cikin shekaru 3 bayan barkewar cutar ta COVID-19, an samu duk nau’ikan kwayoyin cutar a kasar Amurka, inda ta kasance daya daga cikin kasashe mafi samun kwayoyin cutar a duniya. Alkaluman cibiyar dakile da kandagarkin cututtuka ta kasar Amurka sun nuna cewa, a halin yanzu cutar COVID-19 ta nau’in XBB.1.5 na yaduwa cikin sauri a kasar, wadda ta zama kwayar cuta ta farko da mutane mafi yawa suka kamu da ita a Amurka. Fiye da kashi 43 cikin dari na mutanen da suka kamu da cutar COVID-19 sun kamu da nau’in kwayar cutar. A halin yanzu dai, an samu irin kwayar cutar a kasashe da yankuna a kalla 40 a duniya. (Zainab)