logo

HAUSA

Ghana: An tsawaita wa’adin musayar darajar takardun lamuni

2023-01-17 11:24:11 CMG Hausa

Ma’aikatar kudi ta Ghana, ta sanar da sake tsawaita wa’adin shirinta na bayar da damar yin musayar darajar takardun lamuni na cikin gida, da nufin rage yawan bashin kasar, da tabbatar da daidaito a fannin.

Ma’aikatar kudin kasar ta fitar da sanarwa, mai dauke da umarnin dage wa’adin musayar lamunin, daga jiya Litinin 16 ga wata zuwa 31 ga watan, domin baiwa masu ruwa da tsaki damar kara fahimtar inda aka sanya gaba.

Sanarwar dai ita ce irinta ta 3 da ma’aikatar ta fitar, game da shirin da aka ce ya gamu da rashin nasara, bayan da a baya aka kara wa’adinsa a karon farko, daga ranar 30 ga watan Disambar bara zuwa 6 ga watan Janairun nan. Kana an sake dage wa’adin daga 6 ga wata zuwa jiya Litinin, kafin sake dagewa a karo na 3.

Sanarwar da ma’aikatar kudin kasar ta Ghana ta fitar, ta ce za a yi amfani da wannan dama ne domin tattaunawa da dukkanin sassan masu ruwa da tsaki, musamman ma mamallaka takardun lamuni a kasar, ta yadda za a kai ga dakile fuskantar duk wani mummunan yanayi, yayin da kasar ke fafutukar shawo kan kalubalen tattalin arziki.

Kafin sanarwar, a Jumm’ar makon jiya, shugaban masu rinjaye na majalissar dokokin kasar Osei Kyei Mensah-Bonsu, ya yi kira ga ministan kudin kasar da ya zurfafa tuntubar dukkanin masu ruwa da tsaki, game da shirin musayar lamuni a kasar, domin baiwa kowa damar kara fahimtar shirin. (Saminu Alhassan)