Bayern Munich ta sha alwashin cika burikan ta a kakar wasa ta bana
2023-01-19 14:54:13 CMG HAUSA
Rahotannin baya bayan nan na cewa, babban daraktan kungiyar kwallon kafar Bayern Munich na kasar Jamus Hasan Salihamidzic na shan kiraye kiraye ta wayar tarho, musamman a baya bayan nan. Salihamidzic ya ce yawan kiran da yake samu ta wayar sa, sun tilasa shi yawo da batiran waya da dama, domin kaucewa karewar caji a waya.
A baya bayan nan dai kungiyar na cike da ayyuka daban daban, bayan dawowa daga hutun bazara da kungiyar ta yi a Qatar, bayan ta buga wasan atisaye da kungiyar RB Salzburg a ranar 13 ga watan Janairu, karkashin jagorancin koci Julian Nagelsmann.
Kungiyar Bayern Munich na kara shirin tunkarar kakar wasa ta 2022 zuwa 2023, a gabar da take kokarin nema wanda zai maye gurbin kyaftin din ta, kuma babban mai tsaron gidan ta Manuel Neuer.
Kungiyar wadda ta lashe kofunan kwallon kafa da dama, ciki har da na zakarun turai na shekarar 2020 da kungiyar ta lashe, a yanzu tana shirin kashe miliyoyin kudade domin sayo mai tsaron gida, wanda hakan ke nuni ga muhimmancin da kungiyar ke dorawa ga burin ta, na sake lashe kofin zakarun kasar Jamus, wanda zai ba ta damar kaiwa ga nasarorin da ta sanya gaba.
Kungiyar Bayern Munich, ta fara da wasa da RB Leipzig, za ta kuma fuskanci sauran kulaflika 16 da za ta fafata tare da su, a gasar zakarun turai ciki har da PSG ta birnin Paris, ba tare da yin kasa a gwiwa ba.
A dukkanin wasanni 2, Bayern na bukatar ‘yan wasan ta su kasance cikin yanayi mai kyau domin cimma nasara. Don haka, kungiyar na yin duk mai yiwuwa, wajen tabbatar da samun nasara. Da yawa na fatan ganin Bayern ta gaggauta sanya hannu kan kwangilar dauko dan wasan kasar Switzerland Yann Sommer daga Moenchengladbach, wanda ke cikin ‘yan wasan kungiyar sa mafiya kwarewa, tsakanin ‘yan wasa masu buga wannan gasa.
Sai dai duk da yanayin da kungiyar ke ciki, ana sa ran mai tsaron gida Neuer mai shekaru 37, zai kawar da damuwar da wasu ke nunawa cewa zai koma Bayern, zuwa bayan lokacin zafi dake tafe, bayan ya kammala jinyar karaya a kafa da yake fama da ita.
A cewar babban kocin kungiyar Julian Nagelsmann "Nemo mai tsaron gida mai kwarewa ya zamewa kungiyar mu tilas, duk kuwa da irin wahalar da za mu iya fuskanta yayin da muke kokarin cimma nasarar hakan. Ba zai yiwu mu dogara kan mai tsaron gidan mu na 2 ba wato Sven Ulreich".
Kungiyar Bayern tana nazarin makomar ta, tun bayan da ‘yan wasan ta da dama suka hadu da rashin nasara, a gasar cin kofin duniya na kasar Qatar, lokacin da suka bugawa kungiyar kasar Jamus wasa, kuma aka fitar da kungiyar ta Jamus daga gasar tun a zagayen farko na gasar ta hukumar FIFA ta shekarar 2022.
Hakan ya yi daidai da ra’ayin dan wasa mai tsaron bayan kungiyar ta Bayern Joshua Kimmich, wanda ya ce “Ya wajaba hankula su koma ga fuskantar kalubalen dake fuskantar kungiyar mu. Koma bayan da muka samu yayin gasar cin kofin duniyar ya zama wata zaburarwa gare mu, domin mu kara kaimin cimma burikan mu. Aniyar mu ita ce ci gaba da kwazo kamar yadda muke yi kafin zuwan mu gasar cin kofin duniya na Qatar. Ina jin karfin halin ci gaba daga wannan gaba. Kasancewa ta tare da ‘ya’ya na guda 3, ya share mun hawayen bakin cikin dana yi fama da shi, na rashin nasara a gasar ta cin kofin duniya”.
Kimmich mai shekaru 27 a duniya, ya bayyana muhimmancin aiwatar da dukkanin matakai na cimma nasara ba tare da jan kafa ba.
Sai dai fa duk da wannan aniya ta kungiyar Bayern, ta cimma nasarar lashe gasannin dake gabanta, akwai kuma batun nemo karin kudade, domin sayo mai tsaron gida kwararre, wanda hakan shi ma batu ne mai jan hankali.
Ya zuwa yanzu dai, a mahangar koci Nagelsmann, abun farin ciki ne zuwa tsohon dan wasan bayan kungiyar Ajax Daley Blind kungiyar ta su, amma a hannu guda, yana da bukatar samo masu maye gurbin ‘yan wasan sa, da suka hada da Lucas Hernandez, da Noussair Mazraoui, da Sadio Mane.
Yayin da aka riga aka ajiye Hernandez gefe guda, har zuwa karshen kakar wasa ta bana, sabosa ciwo da ya samu a gwiwar sa, kungiyar na fatan tauraron ta dan asalin kasar Senegal wato Sadio Mane, zai dawo taka leda kafin wasan su da PSG.
Dawowar dan wasan kungiyar ta Bayern dan asalin kasar Morocco wato Mazraoui kuwa babu tabbas, saboda ciwon da yake fama da shi mai alaka da kumburi a zuciya, bayan ya yi fama da cutar COVID-19.