logo

HAUSA

WHO ta yabawa gwamnatin Sin bisa kokarinta na tinkarar yaduwar cutar COVID-19

2023-01-16 22:25:26 CMG Hausa

A yau ne kakakin ma’aikatar harkokin wajen kasar Sin Wang Wenbin, ya yi bayani game da abubuwan da aka tattauna tsakanin bangaren Sin da babban direktan hukumar kiwon lafiya ta duniya WHO, Tedros Adhanom Ghebreyesus, ta wayar tarho.

Wang Wenbin ya ce, sakatariyar hukumar WHO da kuma malam Tedros Adhanom Ghebreyesus, sun yabawa gwamnatin kasar Sin domin ta yi kokarin tinkarar yaduwar cutar COVID-19, inda suka godewa bangaren kasar Sin bisa musayar fasahohin yaki da cutar da gabatar da bayanai game da batun ga hukumar WHO. A cewar kakakin, bangarorin biyu sun amince da kara yin hadin gwiwar musayar fasahohin yaki da cutar don tabbatar da kiwon lafiyar duk duniya baki daya. (Zainab)