logo

HAUSA

Gwamantin Saudiya tayi sassauci kan farashin daukar dawainiyar Alhazan Najeriya a aikin hajjin bana

2023-01-16 10:29:10 CMG Hausa

A ranar lahadi 15 ga wata hukumar lura da aikin hajji a tarayyar Najeriya ta kulla yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin ta da kamfanin kasar Saudiya dake lura da daukar dawainiyar alhazai `yan Africa idan sun isa Makka.

Ita dai wanann yarjejeniya ta kunshi kara inganta nau`in abincin da ake baiwa alhazan Najeriya yayin da suke a can kasar Saudiya tare da ragin kashi 5 na kudin abincin da `yan Najeriya zasu biya a aikin hajjin wannan shekara.

Daga tarayyar Najeriya wakilin mu Garba Abdullahi Bagwai ya aiko mana da rahoto.

An sanya hannu kan yarjejeniyar ce a Jeddah dake kasar Saudiya, wanda wannan na daya daga cikin shirye shiryen da kasashen duniya ke yi tunkarar aikin hajjin shekara ta 2023.

Batun aikin bayar da shawarwari ga alhazai da kuma sha`anin sufurin su zuwa wuraren ibada yayin da suke kasar ta Saudiya na daga cikin batutuwan dake kunshe cikin kunshin yarjejeiyar.

A jawabin daya gabatar jim kadan da sanya hannun kan daftarin yarjejeniyar, shugaban hukumar lura da aikin hajji ta tarayyar Najeriya Alh. Zikrullah Kunle Hassan yace hakika aikin hajjin daya gabata na 2022 Najeriya bata ji dadin yadda aka tafiyar da tsarin ba wanda hakan ya haifar da kalubale da dama daga alhazai `yan Najeriya da suka samu damar zuwa kasar ta Saudiya, inda yayi fatan wannan yarjejeniya zata kawar da sake cin karo da irin wadannan matsaloli musammam ma ta fuskar abinci da kuma bandakuna a Muna.

“Muddin dai wadannan tsare-tsare da kukayi ya zama tabbatacce to babu shakka hukumar aikin hajji ta tarayyar Najeriya ta kafa abin tarihi, ba wai kawai ga talakawa masu niyar zuwa aikin hajji ba harma da ita kanta gwamnati,zamu isar da dukkan wadannan bayanai naku ga gwamnati.domin abin da idon mu ya gane mana yanzu ya gamsar damu, kuma bama fatan ya sauya. Muna fatan wanann kamfani na gwamnatin Saudiya mai lura da dawainiyar mahajjata zai aiwatar da dukkannin tsare-tsaren sa a aikace”

A jawabin sa, shugaban kamfanin lura da dawainiyar Alhazai yan Afrika na kasar Saudiya Ahmad Sindy, ya tabbatar dacewa abin daya faru na rashin jin dadi ga alhazan Najeriya  shekarar bara ba zai sake faruwa domin yanzu kasar Saudiya ta kara bijiro da wasu sabbin matakai na kyautata jin dadin mahajjata a bana tun daga saukar su a kasar har zuwa lokacin da zasu koma kasashen su.

Yace yanzu haka an debo kwararru masana akan harkar cimakar dan adam wanda dasu ne za a rinka sarrafa abincin da za a rinka baiwa alhazai yayin da suke a Muna da filin Arfa, kuma an samar da jami`an kiwon lafiya da zasu rinka sanya idanun kan nau`in abincin don tabbatar da ingancin sa .(Garba Abdullahi Bagwai)