logo

HAUSA

Qin Gang da babban sakataren AL sun yi kira da a gaggauta aiwatar da sakamakon taron Sin da kasashen Larabawa

2023-01-16 10:11:58 CMG Hausa

      

Ministan harkokin wajen kasar Sin Qin Gang, da babban sakataren kungiyar kasashen Larabawa ta AL Ahmed Aboul Gheit, sun yi kira da a gaggauta aiwatar da sakamakon da aka cimma, yayin shawarwari tsakanin shugabannin Sin da kasashen Larabawa da ya gabata.

Da yake bayyana matsayar kasar Sin kan hakan a jiya Lahadi, Qin ya ce kasar sa a shirye take ta yi aiki tare da kasashen Larabawa, wajen aiwatar da kudurorin da sassan biyu suka amincewa, bisa ruhin kawancen dake tsakanin su, da gaggauta aiwatar da manyan shawarwarin hadin gwiwar nan 8 da aka gabatar yayin wancan taro, ta yadda hakan zai amfani sassan biyu.   

Kaza lika, Qin ya tabbatar da aniyar Sin ta karfafa hadin gwiwa da kungiyar AL, ta fuskar hada karfi da karfi don kare hakkoki, da halastattun moriyar kasashe masu tasowa, da kare gaskiya da adalci a harkokin kasa da kasa.

A nasa bangare kuwa, Gheit godewa kasar Sin ya yi, bisa tsawon lokaci da ta shafe tana goyon bayan adalci a harkokin da suka shafi kasa da kasa, da goyon bayan ci gaban kasashen Larabawa, da hadin kan kungiyar AL, da taimakawa kasashen wajen yaki da annobar COVID-19.

Bugu da kari, manyan jami’an biyu, sun yi musayar ra’ayi kan karin wasu batutuwan dake jan hankalin kasashen su. (Saminu Alhassan)