logo

HAUSA

‘Yan sanda sun kubutar da mutane 12 da aka yi garkuwa da su a Edo

2023-01-16 10:35:54 CMG Hausa

Rahotanni daga tarayyar Najeriya na cewa, ‘yan sandan kasar sun yi nasarar kubutar da mutane 12, da wasu mahara suka yi garkuwa da su daga tashar jirgin kasa ta jihar Edo dake kudancin kasar.

Da yake tabbatar da hakan cikin wata sanarwa, kwamishinan rundunar ‘yan sandan jihar ta Edo Mohammed Dankwara, ya ce rundunar hadin gwiwar jami’an tsaro ta yi nasarar hakan ne, yayin wani farmakin da ta kai maboyar ‘yan bindigar dake cikin dajin Igboha a jiya Lahadi.

Mohammed Dankwara, ya kara da cewa, mutanen da aka ceto na cikin jimillar wadanda ‘yan bindigar suka yi garkuwa da su, daga tashar jirgin kasa ta Igueben mako guda da ya gabata.

Dankwara ya ce an yi nasarar ceto mutanen 12 lami lafiya. Kuma ya zuwa yanzu, adadin wadanda aka ceto sun kai mutane 18, bayan ceto wasu mutanen 6 a ranar Litinin din makon jiya.  (Saminu Alhassan)