logo

HAUSA

An gudanar da taron ’yan jarida na shirye-shiryen bikin sabuwar shekarar Sinawa

2023-01-16 12:53:12 CMG Hausa

Babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin ko CMG ya gudanar da taron ’yan jarida game da shirye-shiryen bikin murnar sabuwar shekarar Sinawa a yau Litinin, inda aka gudanar da wasu sabbin kirkire-kirkire na fasahohi, aka kuma fitar da sakon rediyo na talla, game da shirye-shiryen bikin sabuwar shekara, da kuma gajeren sakwannin rediyo game da mutum-mutumin mascot na zomo, wato “Tu Yuanyuan”.

Shirye-shiryen bikin murnar sabuwar shekarar Sinawa na bana, zai nuna sakamakon da CMG ya samu wajen gina tsarin fasahohin “5G+4K/8K+AI”, kana za a yi amfani da sabbin fasahohi kamar 4K/8K, da AI da XR da dai sauransu.

Kaza lika za a ci gaba da inganta hadawa, da kirkiro “tunani da zane-zane da fasahohi, wato AI”, da kuma gabatar da shirye-shirye dake da tunani da zane-zane, da fasahohi, da kuma cikakkun kimiyya ga Sinawa na duk duniya.

Tashoshin talibijin na Turanci, da Sifaniyanci, da Faransanci, da Larabci da yaren Rasha, da kuma sabbin kafofin watsa labarai ga kasashen waje, na harsuna 68, da suka hada da kafofin watsa labarai 700 na kasashe da yankunan duniya fiye da 170, za su watsa wannan bikin murnarsabuwar shekarar Sinawan kai tsaye. (Safiyah Ma)