logo

HAUSA

Shugaban Kasar Sin Ya Yi Kira Ga Wadanda Ba Mambobin CPC Ba Su Jajirce Wajen Hidimtawa Muradun Kasar

2023-01-16 20:45:40 CMG HAUSA

Sakatare janar na kwamitin tsakiya na JKS Xi Jinping, ya yi kira ga wadanda ba mambobin jam’iyyar ba, su yi kokarin sauke nauyin da aka rataya a wuyansu ta hanyar jajircewa da kara taka rawa wajen hidimtawa muradun kasa.

Xi Jinping wanda shi ne shugaban kasa, kuma shugaban rundunar sojin kasar, ya bayyana haka ne yayin da ya halarci taron shekara-shekara, na wadanda ba mambobin JKS ba, a babban dakin taron jama’a, gabanin bikin bazara ta kasar Sin ko sabuwar shekarar gargajiya ta Sinawa. (Fa’iza)