logo

HAUSA

Mutane 10 sun mutu sanadiyyar hatsarin mota a kudu maso yammacin Nijeriya

2023-01-15 16:02:57 CMG HAUSA

 

Mutane 10 sun mutu sanadiyyar kwacewar wata motar bus dake gudun wuce sa’a, inda ta shigewa wata babbar mota dake tsaye, a kan babbar hanyar jihar Ogun.

Shugaban hukumar kiyaye haddura ta kasar a jihar Ogun, Ahmed Umar, ya shaidawa manema labarai a Abeokuta, babban birnin jihar cewa, mutane 19 ne hatsarin ya rutsa da su, inda biyu daga cikinsu suka ji raunuka. Hatsarin ya auku ne jiya Asabar, a kan babbar hanyar garin Oniworo dake jihar Ogun.

A cewar Ahmed Umar, babbar motar ta samu matsala ne inda ta tsaya a kan titi ba tare da sanya wata alama ta ankarar da motoci masu tahowa ba, yayin da ita kuma motar bas ta kwacewa direbanta saboda gudun wuce sa’a, har ya shigewa babbar motar dake tsaye.

Ya kara da cewa, dukkan mutanen da suka rasa rayukansu sun mutu ne nan take a wurin, yayin da aka garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti mafi kusa.

Tukin ganganci da lodi fiye da kima da lalatattun tituna ne ke haifar da galibin munanan hadduran da ake samun rahotonsu a kasar. (Fa’iza Mustapha)