logo

HAUSA

Philadelphia na Amurka ya nemi gafara kan gwaje-gwajen likitanci maras da’a da aka yi kan ‘yan asalin Afirka

2023-01-15 17:14:02 CMG Hausa

Kwanan baya mahukuntan birnin Philadelphia na kasar Amurka sun nemi gafara a hukumance kan gwaje-gwajen likitanci da aka yi a wani gidan kurkuku a karnin da ya gabata, inda yawancin wadanda aka yi gwaje-gwajen kansu, maza ne ‘yan asalin Afirka.

Bisa sanarwar da mahukuntan Philadelphia suka bayar, an ce, daga shekarun 1950 zuwa na 1970, da gangan aka bar fursunoni a wurin dake da magunguna masu guba, da kwayoyin cuta, da sauran abubuwan da suke lahanta lafiyar mutane a gidan kurkuku na Holmesburg. Yawancin wadanda aka yi musu hakan, ‘yan asalin Afirka ne maza, da yawa daga cikinsu jahilai ne, wadanda suke jira a yanke musu hukunci, tare da neman tattara kudi don ba da beli.

Sanarwa ta ayyana lamarin a matsayin wani abin bakin ciki na daban,  inda aka yi wa ’yan kabilu wadanda ba fararen fata ba gwaje-gwajen likitanci maras da’a a tarihin Amurka.

An ruwaito cewa, Albert Kligman, masani daga jami’ar Pennsylvania ta Amurka ne ya gudanar da wadannan gwaje-gwaje marasa da’a da muka ambata a baya. Wadannan gwaje-gwaje sun shafi ciwon fata, harhada magunguna, da sarrafa sinadaran halittu, wadanda aka yi wa fursunoni masu yawa kufai da kuma barinsu su yi fama da matsalolin lafiya a duk tsawon rayukansu. Albert Kligman ya rasu ne a shekarar 2010. A shekarar 2021, jami’ar Pennsylvania ta ba da sanarwar neman gafara, tare da goge sunan Albert Kligman daga takardar sunayen mutanen da jami’ar ta ba su lambar yabo.

Ban da haka kuma, bayanan tarihi sun shaida cewa, hukumomin kula da lafiyar al’umma na Amurka sun fara hada hannu da kwalejin Tuskegee a jihar Alabama tun daga shekarar 1932, inda aka tattara daruruwan Amurkawa ‘yan asalin Afirka don gudanar da gwaji kansu dangane da cutar kabba da kuma illolin da cutar ke yi wa lafiyar mutane, amma ba a bai wa wadannan ‘yan asalin Afirka magani yadda ya kamata ba. Bayan shekaru 40, an sa aya ga wannan gwaji. Fadar gwamnatin Amurka White House ta ba da sanarwar shugaba ta neman gafara kan lamarin.  (Tasallah Yuan)