logo

HAUSA

Jarin Kasar Sin Kan Ababen More Rayuwa Ya Gaggauta Ci Gaban Nahiyar Afrika

2023-01-15 17:10:19 CMG HAUSA

An bayyana karuwar jarin kasashen yammacin duniya a kasashen Afrika, a mastayin abun da ya tabbatar da sahihancin tsarin hadin gwiwar kasar Sin da kasashen Afrika, wanda ya fi mayar da hankali kan ababen more rayuwa, kuma ya haifar da ci gaba a fadin nahiyar.

Ovigwe Eguegu, dan Nijeriya, kuma manazarci a cibiyar tuntuba ta raya kasa da kasa ta Development Reimagined, shi ne ya bayyana haka, lokacin da yake tattaunawa da gidan talabijin na kasar Sin CGTN a baya-bayan nan, inda ya yi watsi da zarge-zarge marasa tushe da wasu kafafen yada labarai na yammacin duniya ke yadawa game da kasancewar Sin a Afrika, wanda suke wa lakabi da “Tarkon Bashi”.

A cewarsa, wannan na zuwa ne yayin da Sin ke zaman babbar mai zuba jari a Afrika. Kuma karuwar cinikayya da jari, za su ci gaba da kasancewa muhimmai wajen samar da guraben ayyukan yi da ci gaba da dunkulewar tattalin arzikin duniya. Ya ce galibin kayayyakin more rayuwa da suke taimakawa wajen sauyawa da raya nahiyar, kasar Sin ce ta samar da kudin aiwatar da su.

Ya kara da cewa, kasashen Afrika sun gane cewa, jarin da Sin ke zubawa kan ababen more rayuwa na yin kyakkyawan tasiri ga ci gaban nahiyar. Kuma ba kasashen Afrika ne kadai suka fahimci hakan ba, domin tsare-tsare kamar na hadin gwiwar samar da ababen more rayuwa da zuba jari na duniya karkashin kungiyar G7, wato PGII, da shirin Global Gateway na kungiyar Tarayyar Turai EU, dukkansu sun zo ne bayan gabatar da shawarar Ziri Daya Da Hanya Daya ta kasar Sin.

A ganin manazarcin, kasashen yamma sun gabatar da wadancan shirye-shirye 2 ne saboda sun ga kyakkyawan tasirin da zuba jari kan ababen more rayuwa ya haifar a kasashe masu tasowa, yana mai cewa, hakan, ya tabbatar da sahihancin dabarun kasar Sin. (Fa’iza Mustapha)