logo

HAUSA

Kokarin baiwa jama'ar kasar Sin damar saduwa da danginsu lafiya

2023-01-14 19:28:07 CMG Hausa

A cikin shirin yau, za mu mai da hankali kan yadda kasar Sin ke kula da dimbin zirga-zirgar jama'a a lokacin da bikin bazara ke karatowa.

Ranar 22 ga watan Janairun da muke ciki, bikin bazara ne na kasar Sin. Bikin bazara shi ne farkon shekara da aka kayyade bisa kalandar gargajiyar kasar Sin, kuma shi ne biki mafi muhimmanci a zukatan Sinawa. Bisa al'ada, dole ne dukkan mutane su hadu da dangoginsu a wannan lokacin, kuma su yi bikin murnar sabuwar shekara cikin farin ciki tare. Saboda haka, kewayowar bikin bazara na kowace shekara shi ne lokacin da ake samun kwararar mafi yawan jama'a a nan kasar Sin. (Bello Wang)