logo

HAUSA

Ya kamata Amurka wadda ta fi yada cutar COVID-19 ta bayyana alkalumanta kan yanayin yaduwar cutar

2023-01-14 21:18:33 CMG Hausa

A halin yanzu, sabon nau’in kwayar cutar numfashi ta COVID-19 wato XBB.1.5 na ci gaba da yaduwa a kasar Amurka, wadda ta haifar da sama da kashi 43 bisa dari na yawan mutanen kasar da suka kamu da cutar.

Alkaluman GISAID wadda ke nuna yadda cutar mura ke yaduwa a duk fadin duniya sun ce, a shekaru uku da suka wuce, kusan dukkan nau’ikan cutar COVID-19 sun taba yaduwa a kasar Amurka. To, ina dalilin da ya sa ake yawan samun sauye-sauyen nau’ikan kwayar cutar COVID-19 a Amurka? Ina dalilin da ya sa nau’in cutar wato XBB.1.5 ke kara yaduwa a Amurka? Daya daga cikin muhimman dalilai shi ne, Amurka ta kan yi rufa-rufa game da bayanan yanayin yaduwar cutar.

A shekaru ukun da suka gabata, sassan kasa da kasa sun sha zargin Amurka, sakamakon yadda ta nuna alkaluman bogi, ko kuma ba ta bayyanawa duniya sosai ainihin yanayin yaduwar cutar a kasar. Amurka ta yi ta siyasantar da harkokin cutar, kuma tana yunkurin boye wani abu, da kuma yin gyare-gyare kan ainihin alkaluman cutar, shi ya sa cutar take kara ta’azzara a kasar, abun dake kawo babban tsaiko ga kokarin dakile yaduwar cutar a duk duniya.

A daya bangaren kuma, hukumar WHO ta ce, nau’in XBB.1.5 na cutar COVID-19 yana da karfin yaduwa sosai, ta yadda yake kara janyo harbuwar mutane da dama. Don haka ya kamata Amurka ta bayyana alkaluman yanayin yaduwar cutar a kasar a fili, ba tare da yin rufa-rufa ba, don duk duniya tana da ikon fahimtar gaskiyar lamarin! (Murtala Zhang)