logo

HAUSA

An bude gasar kwallon kafa ta ‘yan kwallon dake buga wasa a kulaflikan gida na kasashen Afirka

2023-01-14 15:28:14 CMG Hausa

A jiya Juma’a ne aka bude gasar kwallon kafa ta ‘yan wasa dake taka leda a kulaflikan gida, na kasashen nahiyar Afirka ko CHAN a takaice. A wasan farko na gasar da aka buga a filin wasa na Nelson Mandela dake yankin Baraki, na kudancin birnin Algiers, mai masaukin bakin gasar Algeria ta doke Libya da ci 1 da nema.

Firiministan Algeria Ayman Ben Abderrahmane ne ya kaddamar da bude gasar, a bikin da ya samu halartar manyan kusoshi a harkar wasanni daga sassan kasa da kasa, da manyan ‘yan kwallon duniya, ciki har da shugaban hukumar FIFA Gianni Infantino, da shugaban hukumar kwallon kafar Afirka CAF Mr. Patrice Motsepe.

Gasar da ake bugawa duk bayan shekaru 2, a wannan karo za ta gudana ne tsakanin ranaikun 13 ga watan nan na Janairu zuwa 4 ga watan Fabarairu. An kuma fara gudanar da ita ne a kasar Kwadebuwa, a shekarar 2009. (Saminu Alhassan)