logo

HAUSA

Amurka, kasar da ke kawo cikas ga kokarin duniya na shawo kan annobar Covid-19

2023-01-14 18:56:38 CMG Hausa

Daga Lubabatu Lei

 Annobar Covid-19 matsala ce da ke addabar duniya baki daya, wadda ke bukatar hadin gwiwar kasa da kasa don shawo kanta. Sai dai abin takaici shi ne, cikin shekaru uku da suka wuce, kasancewarta babbar kasa mafi karfi a duniya, Amurka ta yi ta kawo cikas ga kokarin kasa da kasa na shawo kan cutar, a maimakon daukar nauyin da ke rataye a wuyanta.

A matsayinta na kasa mai ci gaban aikin kiwon lafiya a duniya, mahukuntan kasar ta Amurka ba su dauki matakan da suka kamata ba na tinkarar annobar, inda suka yi biris da lafiyar al’umma da rayukansu, kuma a maimakon haka, sai suka mai da hankali a kan siyasantar da annobar, matakin da ya sabbaba saurin yaduwar annobar.A cikin shekarun uku da suka wuce, an samu yaduwar kusan dukkanin nau’o’in cutar Covid-19 a kasar, inda sama da ’yan kasar miliyan 100 suka harbu da cutar, baya ga kuma sama da miliyan daya da suka rasa rayukansu. Ban da haka, gwamnatin kasar ba ta dauki mataki na kayyade harkokin fita daga kasar ba, inda ta bar cutar ta rika yaduwa zuwa sauran sassan duniya. Alkaluman da aka samar sun yi nuni da cewa, daga watan Afrilun shekarar 2020 zuwa watan Maris na shekarar 2021, gaba daya al’ummar kasar miliyan 23 da dubu 195 suka fice daga kasar, wadanda suka tafi sassa daban daban na duniya. Sa’an nan, yadda kasar ta tilastawa bakin haure da su koma kasashensu na asali ba tare da lura da yanayin lafiyarsu ba, ya kara tsananta yanayin annobar da kasashen Latin Amurka ke ciki.

A yayin da duniya ke kokarin shawo kan annobar, kasar Amurka ta kuma fice daga hukumar lafiya, baya ga tara dimbin rigakafin cutar a gida, ba tare da raba su ga sauran kasashe masu bukata ba. Alkaluman da cibiyar kandagarkin cututtuka ta Amurka ta samar sun shaida cewa, daga watan Maris zuwa watan Satumban shekarar 2021, Amurkar ta bata a kalla rigakafi miliyan 15.1. Idan ba a manta ba, Amurka ta tura rigakafin da lokacin aikinsa ya kusan karewa zuwa kasashen Afirka, matakin da ya jawo suka daga kasashen.

In mun waiwayi tarihi, sau tari mabambantan annoba sun haifar da munanan hasarori ga ’yan Adam, kuma tarihi ya shaida cewa, cuta ba ta san iyaka ko kabila ba. Shekaru ukun da suka wuce da ake yaki da cutar Covid-19 ma sun shaida mana cewa, ’yan Adam makomarsu daya ce, kuma siyasantar da annobar ba zai haifar da komai ba illa lalata hadin gwiwar kasa da kasa wajen dakile cutar, tare da haifar da karin hasarori ga al’ummar duniya.  (Mai Zane: Mustapha Bulama)